Tuesday, 10 July 2018

Neymar ya sha ruwan Allah wadai saboda abinda yayi a filin jirgin saman Brazil bayan dawowa daga kasar Rasha

Bayan da ya sha suka daga masoya kwallon kafa da dama a gasar cin kofin Duniya saboda kwanciyar da ya rika yi da an tabashi, tauraron dan kwallon kafar kasar Brazil, Neymar ya kuma sake batawa masoyanshi rai bayan koma gida daga kasar Rasha.


AS ta ruwaito cewa, dubban mutanene suka taru a filin jirgin saman kasar Brazil cikin doki dan su tarbi tawagar 'yan kwallon da suka dawo daga kasar Rasha amma shi Neymar daya sauka a jirgi, sai ya zagaya ya bi ta kofar baya, inda ba wanda zai ganshi ya fice daga filin jirgin.

Masoya kwallon kafa a kasar da dama abin bai musu dadi ba.

No comments:

Post a Comment