Sunday, 1 July 2018

Pogba da Ronaldo sunyi abubuwan da suka dauki hankulan mutane a wasannin jiya: Anata yaba musu

Bayan ragargazar da kasar Faransa ta wa kasar Argentina jiya a gasar cin kofin Duniya da ci 4-3 wanda ya tilastawa kasar Argentinar ficewa daga gasar, tauraron dan kwallon kasar Faransa, Paul Pogba yayi abinda 'yan kallo da dama suka yabamai.Bayan kammala wasan, 'yan jarida da kyamarorin filin wasan gaba daya suka mayar da hankalinsu kan Messi inda aka nunashi cikin damuwa da takaicin wannan ci da suka sha, sai ga Pogba ya sarkafo hannunshi ta baya ya rungumi Messin inda yake bashi baki/ jajantamai/hakuri akan ibtila'in da ya sameshi.

'Yan kallo da dama sun bayyana wannan abu da Pogba yayi da cewa abu ne me kyau da mutane masu karamcine kawai ke yinshi, da dama sun bayyana Pogba da cewa yana da zuciya me kyau.
Haka shima tauraron dan kwallon kafar kasar Portugal Cristiano Ronaldo yayi abinda akai ta yaba mishi duk da wasu na ganin cewa ba da zuciya da ya yayi ba, Edinson Cavani wanda ya ciwa kasarshi ta Uruguay kwallaye biyun da suka bata nasarar fidda Portugal daga gasar cin kofin Duniya, ya samu matsala inda dole ya fice daga filin wasan ba shiri.

A lokacin da yake fita daga filin wasan anga Cristiano Ronaldo ya kamashi yana taimakamai wajan fita daga harabar filin, wannan abu da Ronaldo yayi yasa 'yan kallo da yawa suka yabeshi da kyawun hali,koda yake akwai wadanda sukace ba da zuciya daya Ronaldon yayi ba, yayi ne kawai dan cavanin yayi sauri ta fita daga filin wasan dan kada ya bata musu lokaci a yayin da suke neman nasara wurjanjan.

No comments:

Post a Comment