Monday, 9 July 2018

R-APC: APC ta kai Buba Galadima kotu

Jam’iyyar All Progressives Congress APC a ranan Lahadi ta ce za ta dau tsattsauran mataki kan shugaban sabuwar jam’iyyar APC, Alhaji Buba Galadima, da sauran mambobin kungiyar.

Babban lauyan jam’iyyar jam’iyyar, Babatunde Ogala, ya bayyana wannan ne a wani jawabi da jam’iyyar ta saki.

Babatunde ya tuhumci Galadima da sauran mambobin R-APC da kokarin satan sunan jam’iyyar, niyyar tayar da hankulan jama’a ta hanyar amfani da sunan jam’iyyar.

Lauyan jam’iyyar yace: “Cin mutuncin da da Mr Galadima yayi da kuma bata sunan APC da ya bata, za mu dauki mataki akanshi da kuma kungiyarsa.”

Game da cewar Ogala, hira da manema labarai da jawabin da Galadima ya saki, tamkar irin jawabin da sojoji suke saki ne lokacin da sukayi juyin mulki.

Ogala ya tuhumci sabuwar APC karkashin shugabancin Buba Galadima a maimakon neman sulhu a kotu.

Yace idan mambobin kungiyar basu jin dadin abinda ya faru a taron gangamin jam’’iyyar APC, su tafi kotu.

No comments:

Post a Comment