Tuesday, 3 July 2018

Real Madrid ta musanta cewa ta sayi Neymar akan kudi Yuro miliyan 310

Da yammacin jiya, Litinin bayan Neymar ya taimakawa kasarshi ta Brazil zuwa wasan dab dana kusa dana karshe a gasar cin kofin Duniya, kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta fito ta karyata wani rahoto dake cewa ta sayi Neymar din akan kudi Yuro miliyan 310.


Sanannen labarine cewa me Real Madrid, Florentino Perez  na yunkurin sayen Neymar din daga PSG, a jiya wani gidan talabijin na TVE ya ruwaito cewa Madrid din ta sayi Neymar akan kudi Yuro miliyan 310 wanda kwantirakin zai kai tsawon kakar wasanni bakwai akan albashi miliyan 45 duk shekara.

Saidai hukumar kungiyar Real Madrid din ta fito tace wannan labari da TVE ta buga karyane su basu sayi Neymar ba kuma sunyi mamakin yanda gidan talabijin din na Sifaniya ya buga wannan labari ba tare da tuntubar wani daga cikin wanda wannan lamari ya shafa ba dan jin gaskiyar labarin, kamar yanda Marca suka ruwaito.

No comments:

Post a Comment