Tuesday, 3 July 2018

Rigimar wa yafi wani tsakanin Ronaldo da Messi ta raba auren wasu masoya

Auren wasu ma'aurata a kasar Rasha ya mutu saboda gardamar data kaure tsakaninsu akan wa yafi wani tsakanin taurarin kwallon kafa, Cristinao Ronaldo da lionel Messi, rigimar ta fara ne tsakanin ma'auratan bayan da mijin me suna Arsen ya tashi Yana murnar cin da kasar Argentina tawa Najeriya.Matarshi dai me suna Lyudmila ta nace akan cewa Ronaldo ya fi Messi, hakan ya hayaka mijin ya kwashe kayanshi daga gidan yafice, kamar yanda jaridar Argumento ta ruwaito ta hanyar The Mirror Uk.

Mijin dai ya bayyanawa jaridar cewa sun hadu da matar tashine a gurin shan giya inda suke kallon kwallon gasar cin kofin Duniya na shekarar 2002, ya kara da cewa tunda aka fara gasar cin kofin Duniyar na 2018 matar tashi take ta aibata Messi tana fadin cewa ko fenareti ya kasa ci a wasansu da kasar Iceland.

Yace ya kasa jure wannan tsiya da matar tashi kewa gwaninshi dan haka shima ya gayamata irin tsanar da yawa banzan Ronaldon da kasarshi, kamar yanda yace, sannan ya kwashe kayanshi ya bar mata gidan, yace shi da ita har abada.

Harma ya kai maganar sakin da zai mata kotu.

No comments:

Post a Comment