Sunday, 15 July 2018

Ronaldo ya isa birnin Turin na kasar Italiya dan kammala komawarshi Juventus

Tauraron dan kwallon kafar Portugal, Cristiano Ronaldo ya sauka a birnin Turin na kasar Italiya a yau, Lahadi inda ake sa ran gobe, idan Allah ya kaimu zai kammala sauran abubuwan da ake bukata dan tabbatar dashi a matsayin dan kwallon Juventus.


Juventus ta sayi Ronaldo akan kudi fam miliyan dari daga Real Madrid bayan da ya shfe shekaru tara a kungiyar, a cikin alkawarin na zuwanshi Juventus, Ronaldo zai rika daukar albashin yuro miliyan talatin a shekara.

Kungiyar ta Juventus ce ta wallafa wannan hoton na Ronaldo a dandalinta na sada zumunta yayin da ya sauka a wani filin jirgin sama na birnin Turin tare da budurwarshi Georgina Rodriguez

No comments:

Post a Comment