Tuesday, 31 July 2018

Sabon kayan maye ya bulla a Ghana

A Ghana, hukumomi sun ce sun bankado yadda masu safarar kwaya ke shigar da wani sabon kayan maye mai suna KHAT cikin kasar da nufin fataucinsa zuwa Amurka da nahiyar Turai.

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Ghana ta ce sabon kayan mayen yana kama da busasshen ganyen zogale kuma yana matukar bugarwa da kama mutum.

Mista Solomon Stanley Eyo, shi ne daraktan ayyuka na hukumar, ya ce sabon kayan mayen na da matukar hadari kamar sauran miyagun kwayoyi da ake ta'ammali da su
A cewar sa, "Ganyen KHAT yana tsirowa ne kamar yadda tabar wiwi ke tsirowa, kuma ana samun sa ne a kasashen gabashin Afrika, kamar Kenya da sauran su, inda mazauna wannan kasashe suke amfani da shi, kuma yana bugarwa ne kamar tabar wiwi sannan kuma tana iya zama jiki ga mai sha."

"Ana shigo da tabar KHAT ne zuwa kasashen Amurka da Burtaniya, amma irin wadannan kasashen sun hana shigar da tabar."

"Saboda haka, kamar yadda masu safarar kwayoyi suke yi domin yaudarar mutane, sai sun fara shigo da ita daga Ethiopia zuwa Ghana sannan kuma sai a yi safarar ta zuwa nahiyar Turai."

Jami'in na hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Ghana ya ce sun shirya yin hadin guiwa da hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya (NDLEA), ta hanyar wani shiri na musamman mai taken 'Operation Eagle 1 da 2' inda suka yi hadin gwiwa da jami'an tsaro na bangaren yaki da miyagun kwayoyi.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment