Friday, 13 July 2018

'Salon kwallon da Faransa ta buga da Belgium abin kunyane'

Wasan daf dana karshe da kasashen Belgium da Faransa suka buga wanda ya kare da sakamakon Faransa na cin Belgium 1-0, be wa da yawa daga cikin 'yan kwallon kasar Belgium din dama wasu 'yan kallo dadi ba.


Kyaftin din Belgium, Eden Harzard ya bayyanawa manema labarai cewa, abin kunyane ace kasa kamar Fransa suna wasan tare gida, Faransa dai bayan kwallon da Umtiti ya ci mata duk sai 'yan kwallon suka koma gidansu suka tare suka bar Kylian Mbappe ya rika amfani da gudunshi wajan kai hari.

Hazard yace, shi dai da yayi nasara da irin salon kwallon da Faransa ta buga musu gara yayi rashin nasara da salon kwallon kasarshi ta Belgium, Hazard dai na daya daga cikin 'yan kwallon da suka haskaka a gasar ta Rasha 2018, kuma salon kwallon kasar shi ta Belgiuma a wannan gasa shine a fita a nemi kwallo kawai.

Me tsaron gida na Belgium din, Thibaut Courtois shima ya soki salon kwallon da Faransar ta buga inda yace wannan kwata-kwata ba kwalloce suka buga ba.

Ya kara da cewa, suna da 'yan cin buga irin salon kwallon da suke so amma hakan ba abu bane me kyan gani ba, kuma basu fimu komi ba.
Daily star.

No comments:

Post a Comment