Saturday, 7 July 2018

Sanata Ndume ya bayyana dalilin da yasa Sanatoci ke jin tsoron Bukola Saraki

Sanata Ali Ndume ya bayyana dalilin daya sa yawancin sanatoci suka zama 'yan amshin shatan kakakin majalisar, Bukola Saraki akan lamurra da yawa, yace da yawan Sanatocin na amincewa da tsare-tsare tare da sarakinne saboda kwadayi.


Ya bayyanawa kamfanin dillancin labaran Najeriya cewa, Sanatocin na matukar tsoron Saraki da binshi sau da kafane saboda tsoron kada su rasa wasu damarmaki da alfarma a majalisar wadda kuma ta hannun sarakin suke biyowa, haka kuma wasu daga cikin Sanatocin saboda gudun mayar dasu saniyar warene a al-amuran majalisar shiyasa suka zama 'yan amshin shata.

Yace da yawan sanatocin basu iya fitowa su fadi gaskiya akan al-amura saboda an mayar da harkar majalisar ta wani mutum daya, kuma idan mutum yayi magana sai a hanashi samun wasu abubuwa na musamman da ake baiwa 'yan majalisar wanda duk suna hannun Sarakine.

No comments:

Post a Comment