Sunday, 8 July 2018

Sanatoci 30 da ‘yan majalisar wakilai 60 zasu tsallaka PDP

Mambobin tsagin R-APC na jam’iyyar APC mai mulki sun kamala shirye-shiryen tsallakawa zuwa jam’iyyar adawa ta PDP nan bada dadewa ba, kamar yadda rahoton jaridar Tribune ya wallafa.


Wata majiya daga cikin tsagin R-APC a majalisar kasa ta shaidawa Tribune din cewar ficewarsu zata kawo canji a kunshin shugabancin majalisun kasar nan. Majiyar ta kara da cewar, ‘yan kwanaki kadan ya rage su fice daga APC.

Majiyar ta bayyana cewar ‘yan majalisar zasu kamala dukkan shiri tare da ficewa daga APC sati daya kafin tafiyarsu hutu ranar 21 ga watan Yuli da muke ciki.

Shugabannin majalisun kasa, Bukola Saraki da Yakubu Dogara, ne ke jagorantar ‘yan majalisun da zasu canja shekar domin ganin cewar sun samu rinjayen da zai basu dammar cigaba da rike mukamansu.

‘Yan majalisar na son kafa hujja da rikicin da ya dabaibaye APC a matsayin dalilinsu na ficewa daga jam’iyyar, kamar yadda yake a kundin tsarin mulkin kasa cewar, dan majalisa zai iya canja sheka ne kawai idan da akwai rabuwar kai ko rikic cikin jam’iyyar day a ci zabe. 

Mambobin majalisar sun fito ne jihohin arewa da suka hada da, Kano, Adanawa, Sokoto, Oyo, Kwara, Kogi, Kaduna, Bauchi, Benuwe da sauran su.

Tsagin R-APCya kunshi mambobin jam’iyyar PDP da suka shiga APC kafin zaben 2015 da kuma wasu ‘yan APC da basa jin dadin yadda tafiyar gwamnatin jam’iyyar tasu ke tafiya.


No comments:

Post a Comment