Sunday, 8 July 2018

Saraki na shirin tsayawa takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP: Cikin Atiku, Kwankwaso da Tambuwal ya duri ruwa

Jim kadan bayan da kotu ta wakeshi daga laifin kin bayyana kadarorinshi da gwamnatin tarayya ke zarginshi da yi rahotanni sun bayyana cewa, kakakin majalisar dattijai Bukola Saraki ya fara shirye-shiryen tsayawa takarar shugaban kasa.


Jaridar The Nation ta bayyana cewa kasa da a wanni 24 bayan da kotu ta wanke Sarakin ya fara tattaunawa da na kusa dashi da kuma wasu manya dan fitowa takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP. Sarakin dai yana cike da takaicin kararshi da gwamnatin tarayya takai Kotu da kuma karin rashin jituwa dake tsakanin bangaren dokoki dana zartarwa.

Wannan labari ya saka tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal cikin rudani, saboda dukkansu ukun suna da niyyar fitowa takarar shugaban kasa kuma a jam'iyyar ta PDP kamar yanda rahotanni suka bayyana.

Saidai wani rahoton na cewa jam'iyyar ta PDP tace ba zata baiwa masu tsallake-tsallake tsakanin jam'iyyu tikitinta na takarar shugaban kasa ba ainihin 'yan jam'iyyar da basu taba canja sheka bane zata baiwa.

A bangaren tsohon shugaban kasa, Obasanjo kuwa, rahotanni sun bayyana cewa saboda son ganin an kawar da Buhari daga mulki, a shirye yake ya goyi bayan duk dan takarar da PDP ta tsayar a matsayin me neman shugaban kasa, koda kuwa Atikune.

No comments:

Post a Comment