Saturday, 7 July 2018

Sheikh Ahmad Gumi ya caccaki gwamnatin Buhari: Yace ko me kula da dakin kurya bata isa ta canjawa Buhari ra'ayiba

A wata hira da jaridar Punch tayi da malamin addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya caccaki gwamnatin shugaba Buhari inda yace babu abinda ta tsinanawa 'yan Najeriya banda kara sakasu cikin kunci.


Da aka tambayeshi me zai hana ya baiwa shugaba Buhari shawara akan yanda za'a warware matsalar Najeriya maimakon caccakarshi?.

Sai ya bayyana cewa ai shi ba ya iya kaiwa dakin kurya kuma ko me kula da dakin kurya ba ta isa ta canjawa Buhari ra'ayiba, ya kara da cewa shifa Buhari kallon duk 'yan Najeriya yake da basu tare dashi a matsayin mutanen banza, barayi masu cin hanci.

Yace Buhari bai cancanci ya mulki Najeriya ba, kowace matsala akwai shugaban da ya dace da ita wanda zai kawo yanda za'a warwareta, dan haka yana kiran Buhari daya hakura ya barwa wani wanda zai iya mulkin kasarnan yazo ya hau.

Yace mabiya Buhari wanda yawanci jahilaine marasa aikin yi ba zasu hanashi fadin gaskiya akan Buharin ba, zai ci gaba da yin bayani har sai randa suka fahimceshi.

Malam ya kuma ce duk da yawan shuwagabannin kasar da yankin Arewa ya samar a kasarnan amma har yanzu yankin ne a baya wajan cigaba, ya dora alhakin hakan akan dabi'ar shuwagabanni na kin son taimakawa na kasa dasu.

Yace har yanzu akwai inda idan kasa kaya masu kyau wai sai ace kana gasa da sarkine, ya kara da cewa ya kamata ace an daina wannan abu, kai harma kwanciyar da ake ana gaishe da sarakuna ya kamata a dena, suma mutanene irinmu, amma suna jin kansu kamar sunfi kowa, inji malam.

No comments:

Post a Comment