Monday, 2 July 2018

Shekau Na Fama Da Matsanancin Rashin Lafiya

Shugaban 'yan ta'adda kuma babban bokan jejin Sambisa yana cikin matsananciyar rashin lafiya, akwai bukatar ya samu kulawan kwararrun likitoci su duba shi amma babu hanya, saboda dakarun sojojin Nijeriya 'yan kundunbala sun tare hanya da dukkan wata mashiga.


Kafin su Albarnawiy su masa tawaye shekarar 2014 lokacin da sukayi hari garin Mubi sun tafi da wasu kwararrun likitoci da suke aikin agaji karkashin majalisar dinkin duniya, likitocin sukan duba babban bokan jejin sambisa tare da amincewar babban likitansa, to halin da ake ciki yanzu gaba daya likitocin sun gudu sun koma bangaren Albarnawi dake da sansani a yankin tafkin Chadi, babu wani kwararren likita da zai duba Boka na Sambisa a halin da ake ciki, ga matsanancin jinya dake damunsa.

Wannan labari ne mai dadi da farin ciki shi ya sa na kasa daurewa na ce bari na sanar da 'yan Nijeriya masu kaunar zaman lafiya don haka mu taya shi da addu'a kada Allah Ya bashi lafiya. Amin.
rariya.

No comments:

Post a Comment