Sunday, 1 July 2018

Shin wa zai gaji Lionel Messi?

Sa'ilin da Messi da Mbappe suka rungume juna bayan karawa tsakanin Faransa da Argentina, sai ya zamanto kamar wata alama ce ta komawar kwarewar Messi kan Mbappe.


Daukacin wadanda suka kalli wasan da aka yi tsakanin Faransa da Argentina na cin kofin duniya a Rasha, sun bar filin wasan tare da yakinin cewa sun kalli wani wasa na musamman, wanda za a dade ana tunawa.

Sannan kuma daya daga cikin 'yan wasan da suka taka leda a filin da ya burge kowa.

Shekarun Kylian Mbappe 19 ne kacal, amma ya samu nasarar zura kwallo biyu a wannan karawa, ya kuma yi wasa mai kayatarwa inda har ya samo wa kasarsa bugun fanareti wanda shi ne ya haifar da kwallo ta farko da aka zura a ragar Argentina, a karawar wadda aka tashi Faransa na da kwallo 4, Argentina na da 3.

Wannan wasa ya fito da kwazon Faransa, kuma ya nuna cewa za ta iya taka muhimmiyar rawa, kila ma ta samu nasarar lashe kofin na duniya a karo na biyu a tarihinta.

Mbappe: Dan wasan gaba da ya hada komai
Mbappe bai zo duniya ba a lokacin da kasarsa Faransa ta lashe kofin duniya, sa'ilin da ta karbi bakuncin gasar a 1998.

An haifi dan wasan ne a ranar 20 ga watan Disamba na shekarar 1998, kuma yanzu haka yana wasa ne a kungiyar Paris St-Germain da ke Faransa, a matsayin aro daga Monaco.
Amma ana sa ran PSG din za ta saye shi kan kudi Fan miliyan 165.7.
Hakan zai sa ya zama dan wasa na biyu mafi tsada a duniya, kasa da yadda PSG din ta sayi dan wasan Brazil Neymar, daga Barcelona a kan kudi Fan miliyan 177.

Mbappe na da hazaka sosai ciki har da tunani cikin hanzari, yana amfani da dukkanin kafafunsa yadda ya kamata, ya iya cin kwallo da ka, yana da kwazo, sannan ya iya hangen inda zai zura kwallo a cikin raga.
Bayan karawar tsakanin Faransa da Argentina, ga abin da tsohon dan wasan Ingila Alan Shearer ya ce game da Mbappe: "A shekara 19, a ce ya yi wasa mai kayatarwa irin wannan a gaban Lionel Messi, yayin da miliyoyin al'umma ke kallo, wannan ba karamar hazaka ba ce."
Shi ne matashin dan wasa mafi karancin shekaru da ya ci kwallo biyu a wasa guda a gasar kofin duniya tun bayan Gwarzon dan wasan Brazil Pele, da ya ci biyu a wasan karshe tsakanin Brazil da Sweden a 1958.


No comments:

Post a Comment