Tuesday, 10 July 2018

Shugaban Turkiyya ya nada surukinsa Ministan Kudi

Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya nada surukinsa a matsayin ministan kudi bayan da ya sha rantsuwar kama aiki na wa'adin shekara biyar.


Nadin Berat Albayrak ya janyo rashin tabbas a kasuwar hannayen jari game da damuwar da aka nuna a kan yadda shugaban kasa ke fifita danginsa kan wasu a harkokin gwamnati.

Mr Erdogan, wanda aka sake zaba a watan da ya gabata, ya sha alwashin "kawo ci gaba a kasar " ta hanyar amfani da sabon ikon da aka ba shi.

Sai dai 'yan adawa na fargabar shugaban kasar zai yi wa mulkin dimukradiya karan-tsaye.

Sabon mukamin Mr Erdogan zai sa majalisar dokoki da kuma ofishin Firai Minista su daina tasiri, wanda shi ne tsarin da ake amfani da shi tun bayan kafuwar kasar a matsayin jamhuriya ta zamani, shekaru 95 da suka gabata.

Mukamin zai ba shi damar nada ministoci da mataimakin shugaban kasa tare da yin katsalandan a cikin harkokin shari'a.

Bayan da ya sha rantsuwa a Majalisar dokoki a ranar Litinin, Erdogan ya fada wa bakin da suka je fadar shugaban kasa da ke Ankara babban birnin kasar cewa, Turkiyya "ta bude sabon babi."

"Za mu daina amfani da tsohon tsarin da a baya ya jefa kasarmu a cikin rikicin siyasa kuma ya janyo koma bayan tattalin arziki," in ji shi.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment