Tuesday, 3 July 2018

Shugaban 'yansanda barawone, ya cinje mana hakkokinmu: Buhari mutumin kirkine>>Inji 'yansandan da sukayi zamga-zanga a Borno

A jiya, Litinin ne 'yan sanda suka fito kan titunan garin Maiduguri suna zanga-zangar rashin biyan su alawus-alawus din su na tsawon watanni bakwai, rahotanni sun bayyana cewa dole harkokin jama'a suka tsaya cik saboda wannan zanga-zanga, haka ma 'yan sandan sun tilastawa wasu daliban makarantun gwamnati shiga ayi zanga-zangar dasu.


Shafin Sahara Reporter ya ruwaito cewa, 'yan sandan sun rika waka suna fadin cewa, shugaban 'yansanda barawone, ya cinye musu kudin Alawus dinsu amma Buhari mutumin kirkine, dole ya ji wannan labari.

Wani dan sanda da baya so a bayyana sunanshi ya bayyanawa Sahara Reporters cewa, watansu bakwai kenan an kawosu  Borno amma ba'a biyasu hakkokinsu ba, yace wasu daga cikin jami'an sun rasa 'ya'yansu saboda basu da kudin da zasu kaisu asibiti.

Ya kara da cewa sojoji ana basu hakkokinsu kuma ana basu abinci sau uku a rana amma su ba labari, sannan kuma shugaban 'yansandan yana sayar da takardar karin girma ga 'yansandan masu hanya.

Sunyi kira da cewa shugaba Buhari ya binciki shugaban 'yansandan saboda cin hanci yake musu a ma'aikatar tasu.

Sahara Reporter ta kuma tuntubi kwamishinan 'yansanda na jihar, Damian Chukwu inda ya shaida musu cewa rashin sakawa kasafin kudin 2018 hannu da wuri shi ya jawo wannan lamari amma hukumar ta san da wannan matsala kuma tana kokarin warwareta.

A jiyane dai hukumar 'yansandan ta fitar da sanarwar cewa, babu wani dan sanda da yayi zanga-zanga a Borno kawai dai sunje ne neman ba'asine akan hakkokinsu cikin lumana.

No comments:

Post a Comment