Sunday, 8 July 2018

Ta fasa aure don mijinta matsoraci ne

Wata amarya a India ta fasa aure don mijinta ya firgita lokacin da wata guguwa ta taso a yankinsu.


Matashiyar ta yanke wannan shawara saniyoyi kalilan gabanin a daura aure,abinda yasa dangin miji da na amarya suka maida filin aure, sansanin yaki ta hanyar dambatawa babu kakkautawa,har ta kai ga zuwan jam'ian tsaro don kwantar da tarzoma.

Lamarin dai ya samo asali ne daga wata guguwar da ta taso, wacce ta firgita ango gaban bainar jama'a,abinda yasa nan take Amarya ta ce sai dai ta mutu ba miji amma ba za ta taba hada jini da shi ba".

Kafar yada labarai ta Ingila The Mirror ce ta rawaito wannan labarin mai ban ta'ajibi.

Lamarin ya afku ne a yankin Bihar da ke gabashin Indiya.

Sidheshwar Azad,wani mai gadi a helkwatar 'yan sandan yankin ya sanar da cewa,an kama 3 daga cikin dangin amarya sabili da mummunar dabi'arsu.
Trthausa.

No comments:

Post a Comment