Sunday, 8 July 2018

TA TILASTA WA MIJINTA YA SAKE TA SABODA KYAWUNSA YA YI YAWA.

Abin mamaki ba ya ƙarewa a Duniya. An datse auren Halima wata mace ce 'yar asalin kasar Saudiyya. Wacce ta ce ta shiga tsaka mai wuya sakamakon kyaun sura da cikar halittar mijinta Muhammad.  Muhammad ma'aikacin banki ne a Garissa.   

Dalilin mutuwar auren nasu ya saɓa daga sauran dalilan mutuwar aure. Ba kamar yadda muka sani ba, mace na neman saki idan mijinta ya gaza kula da hakkokinta na aure ƙkamar ci, sha, sutura, kula da lafiya da sauransu ba. A cewarta, Muhammad,  Allah ya yi masa kyau da farin jini na 'yammata wanda da wuya ya haɗu da mace su rabu lafiya ba tare da ta afka kogin kaunarsa ba. Daga nan sai su fara soyayya. 

A cewar Halima, wannan shi ne babban abinda yake kona mata zuciya. Kuma ya sa zargin mijin nata, ya ɗarsu a zuciyarta A yanzu har ta kai ga ko aiki ya fita ko wata unguwar, in dai ba tare za su je ba; to ta shiga fargabar kada ya kula 'yammata, har sai ya dawo sannan hankalinta yake iya kwanciya.

 Makwabtan su Halima ma sun ba da shaidar yadda mata ba dare ba rana suke kai wa Muhammad caffa. A kan haka ta tattara kayanta ta koma gidan iyayenta. Domin a cewarta tun da ta aure shi shekara guda a haka ake. Gara ya sake ta, da ta zauna a cikin takaicin nan har abada.

SARAUNIYA

No comments:

Post a Comment