Monday, 9 July 2018

Tabbas Ministar kudi ta nemi a bata takardar dauke yin bautar kasa>>inji NYSC

A yayin da batun amfani da takardar boge ta dauke mata yin bautar kasa ke kara daukar hankula, Hukumar kula da aikin bautar kasa, NYSC ta yi magana akan takar dar da aka zargi ministar kudi Kemi Adeosun da amfani da ita.


Jaridar Premium Times ce ta kwarmata wancan labari na takardar Boge.

Amma yanzu jaridar Vanguard ta ruwaito cewa hukumar ta NYSC ta tabbatar da cewa Kemi ta nemi a bata takardar dauke mata yin bautar kasar amma basu bayyana cewa ko an bata takardar ba kokuwa a'a.

Me magana da yawun hukumar Adeyemi Adenike ya bayyana cewa, yanzu abinda ya rage shine su tantance cewa ko an baiwa Kemi takardar dauke yin bautar kasar ko kuwa.

No comments:

Post a Comment