Tuesday, 10 July 2018

Tambuwal ya dora alhakkin kashe-kashe akan gazawar shugabanci

Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya daura hakkin kashe-kashe da ake fama da shi a kasar akan gazawar shugabanci.


A wata sanarwa da ya saki dauke da sa hannunsa a ranar Talata, 10 ga watan Yuli, Tambuwal yace mace-macen abu ne da za’a iya hanawa da kuma dakatarwa.

A cewarsa babu ta yadda Najeriya zata ci gaba a wannan karni na 21 da ake ciki, idan har a kullun za’a ta samun yawan mace-macen al’umma.

Tsohon kakakin majalisar wakilan, yayi ta’aziyya ga iyalan wadanda aka kashe a fadin kasar.

Ya yi Allah wadai da yadda ake kaiwa jami’an tsaro da tshoshinsu hari, cewa wa zai kare al’umma da dukiyoyinsu a kasar a cikin wannan yanayi da ake ciki.

Daga karshe Tambuwal ya jadadda cewa akwai bukatar a sake gina hukumomin tsaron kasat domin yiwa tufkar hanci kan halin da tsaron kasar ke ciki.

No comments:

Post a Comment