Monday, 9 July 2018

Tsohon dogarin Buhari, Jokolo ya soki sarkin musulmi da sarakunan Arewa akan kin yiwa Buhari magana ya saki Dasuki

Tsohon Dogarin Shugaban kasa Muhammadu Buhari a lokacin mulkin Soja Mustapha Jokolo ya soki manyan shugabannin Arewa na yin shiru game da asalin abubuwan da ke aukuwa a Yankin. Jokolo yace dai mutanen Arewa su ke ba da kan su.


Mustapha Jokolo wanda shi ne Dogarin Janar Buhari a baya da yayi mulki yayi kaca-kaca da Sarkin Musulmi da sauran Sarakunan Kasar Arewa inda ya zarge su da munafunci da sakaci kan halin tsaro da rashin adalci da ake yi wa Arewacin kasar.

A wata hira da Jokolo yayi da Jaridar The Sun ne ya bayyana wannan inda yayi magana musamman game da abin da ke faruwa game da tsohon Mai bada shawara kan harkar tsaro Sambo Dasuki. Jokolo yace babu abin da Sultan yayi a kan lamarin.

Al-Mustapha Jokolo ya koka da yadda Gwamnati ta cigaba da rike Sambo Dasuki duk da Kotu sun nemi a sake shi. Jokolo yace ko sau daya Sarkin Musulmi bai taba tara Sarakuna su ka je wajen Shugaba Buhari su na nema ayi wa Dasuki afuwa ba.

Babu dai wani Sarki daga Arewa da ya iya cewa komai duk da irin abin da ya faru da Dasuki. Ana cigaba da daure Sambo Dasuki duk da Kotu ta bada belin sa fiye da sau daya. Jokolo ya nemi a bi umarnin Kotu ko da cewa tayi a harbe tsohon NSA din.


No comments:

Post a Comment