Sunday, 1 July 2018

Wani Fasto mai siyar da tikitin shiga Aljannah ya shiga hannun hukuma

Hukumar yan sanda a kasar Zimbabwe ta kama wani Fasto tare da matarsa inda ake tuhumarsu da sayarwa da jama'a tikitin shiga aljanna.

Faston mai suna Tito ya bayyanawa dubban jama'a cewa Yesu Almasihu ne ya ba shi wannan tikiti domin ya sayar musamman ga wadanda suka kasance masu aikata zunubi domin su ma su samu damar shiga aljannar.

Ya ce "Ban damu da abinda mutane ko jami'an yan sanda ke cewa akai na ba, kawai nasan an kama ni ne saboda ina yin aikin ubangiji. Yesu Almasihu ne ya bayyana a gareni kuma ya bani tikiti tare da shaida min cewar na sayar da shi ga Jama'a domin su samu rabauta".

Yanzu haka dai dubban mutane ne ke yin zanga-zangar nuna adawa da kama Fasto din da aka yi, inda suke kira da hukumar yan sanda tayi gaggawar sakinsa, domin ko ma mai ya faru da kudinsu suke sayen tikitin ba da kudin wani ba.

No comments:

Post a Comment