Thursday, 12 July 2018

Wannan ba shine Buharin da talakawa suka zaba ba a 2015>>Tambuwal

Gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Aminu Tambuwal ya yi tsokaci tare da tambihi mai daukar hankali a game da kashe-kashen da ke aukuwa a kusan dukkan sassan kasar nan inda ya bayyana cewa ba abun da talakawan kasar suka zaba ba kenan a shekarar 2015.


Gwamnan dai ya bayyana hakan ne a lokacin da yake nuna alhinin sa akan mutane sama da 30 da wasu 'yan bindiga suka kashe a kauyen karamar hukumar Rabbah ta jihar Sokoto. 

gwamnan dai ya nuna matukar rashin jin dadin sa game da kisan sannan kuma yayi wa iyalan mamatan ta'aziyya tare da addu'ar samun zaman lafiya a jihar da ma kasar baki daya. 

No comments:

Post a Comment