Monday, 9 July 2018

Wasan Faransa da Belgium: Yanda Thierry Henry ya samu kanshi a tsaka mai wuya

A yayin da kasashen Faransa da Belgium ke shirin buga wasan daf dana karshe a gasar cin kofin Duniya 2018 a kasar Rasha, hankula sun karkatu kan wasan nasu sosai saboda duk kasashe biyun gwanayene a harkar kwallo kuma sun taka rawar gani sosai a gasar ta bana.


Wasu na ganin cewa dai kasashen biyune ya kamata ace sun hadu a wasan karshe na wannan gasar, saidai ba haka abin yazo ba.

Wasu na bayyana wasan na kasashen biyu da cewa zafinshi daidai yake da wasan karshe, dan duk kasar data wuce wannan mataki ana kyautata zaton itace zata lashe kofin, duk da cewa wasa zai iya bada mamaki.

Wani abu dake kara daukar hankulan mutane game da wasan Faransa da Belgium shine yanda tsohon tauraron dan kwallon Faransa, Thierry Henry yake aiki a matsayin me taimakawa me horasa da 'yan wasan kasar Belgium, gashi kuma za'a buga wasa tsakanin kasar da yake wa aiki da kasarshi ta asali, masu sharhi sun bayyana wannan abin da Henry ya samu kanshi a ciki da tsaka mai wuya.

Da yake magana da 'yan jarida, tauraron dan kwallon Faransa, Olivier Giroud ya bayyana cewa abune banbarakwai ace yau gashi zamu buga wasa amma Henry yana bayan abokan hamayyarmu, ya kara da cewa, amma zasu nunawa Henry cewa yayi zaben tumun dare.

Amma dai wasu na ganin cewa Henry zai yi amfani da wannan dama ya nunawa kasarshi cewa ya kawo karfi fa a harkar horas da 'yan kwallo kuma zai iya jagorantar kungiyar 'yan kwallon kasar.

Yanzu dai abin jira a gani shine yaya Henry zai yi da sakamakon wasan?

Gabe, talatane dai za'a buga wannan wasa da misalin karfe bakwai na yamma.

No comments:

Post a Comment