Sunday, 8 July 2018

Wasan Game da ya sa yara 10 kashe kansu a kasar Saudiyya

Karo na biyu kenan da wani matashi ya kashe kansa a tsarkakken birnin Madinah na kasar Saudiyya, bayan ya yi wasan bidiyo na kwamfuta "Blue Whale".


A yanzu haka wasan ya yi sanadiyyar mutuwar yara kusan 10 a kasar.

A ranar Jumma'ar nan da ta gabata ma, wani matashi ya aika kansa lahira bayan da ya yi wannan wasan kai tsaye a yanar gizo.

A cewar Jaridar Saudiyya Sabq, wata matashiya mai shekaru 13 da haifuwa ta kashe kanta kan wannan wasan.

Haka zalika a farkon wannan mako man, wani matashi a yankin Abha ya bakwanci barzahu.

A karo na farko wasan na "Blue Whale" ya bayyana a shafukan sada zumunta na kasar Rasha.

Bayan yara da dama sun mutu bayan da suka yi wannan wasan,sai shugabannin kasar suka dinka yi wa uwayen yara hannunka mai sanda.
trthausa.

No comments:

Post a Comment