Saturday, 7 July 2018

Ya mutu wajan kokarin kwaikwayar yanda Messi yake kwallo

Wani matashi dan kimanin shekaru 19 ya hadu da ajalinshi wajan kokarin kwaikwayar yanda gwaninshi tauraron kwallon kafa, Lionel Messi ke kwallo, matashin me suna Sagar Das ya fadi yayin da ake tsaka da buga kwallo bayan da kwallon ta bugi kirjinshi.

Lamarin ya farune a kasar India kamar yanda times of india ta ruwaito.

Ana tsaka da kwallo sai aka dokowa Sagar kwallon, garin ya kwaikwayi yanda Messi ke cin kwallo sai yayi tuntube kwallon ta daki kirjinshi da karfi ya fadi kasa sumamme, an garzaya dashi asibiti amma daga baya sai ya rasu.

Abokai da makwautanshi sun bayyanashi da cewa yaron kirkine ba ruwanshi da tonon fada, 

'Yan uwanshi sun ce  Sadar yana da son kwallo dan tunda aka fara gasar cin kofin Duniya babu wasan da ya wuceshi dan lokuta da damama baya zuwa makaranta saboda kwallon.

No comments:

Post a Comment