Monday, 9 July 2018

'Yan kasar Jamus sun dorawa Ozil laifin fitar dasu daga gasar cin kofin Duniya: Mahaifinshi yace da shine daina bugawa kasar kwallo zaiyi

Tun kamin zuwan kasar Jamus gasar cin kofin Duniya, tauraron dan kwallonta, Mesut Ozil ya shiga wata harkalla da 'yan kasar bayan da aka ganshi ya dauki hoto da shugaban kasar Turkiyya, Erdogan.


Asalin Ozil dan kasar Turkiyyane, daga can iyayenshi suka zo Jamus, hoton da ya dauka da Erdogan yasa 'yan kasar suke mishi kallon cewa ya nuna kasar Turkiyya yake so ba jamus din ba, wannan lamari ya jawo zazzafan cece kuce wanda har manyan 'yan siyasa suka shiga ciki aka rika bayyana Ozil da cewa yaci amanar kasa.

Fitar da Jamus daga gasar cin kofin Duniya ya kara kazanta wannan lamari inda tun daga fili 'yan kallo suka fara jifar Ozil da kalamai, da yawan 'yan kasar sun bayyana cewa laifin dan wasanne fitar dasu da akayi saboda baya kishin kasar ta Jamus.

Abin yayi kamari ta yanda har me magana da yawun kungiyar kwallon kafar kasar yace da sun sani ma basu zo da Ozil gasar ba.

Haryanzu dai Ozil be mayar da martani akan ko daya daga cikin wadannan kalamai da ake ta gaya mishi ba.

Saidai mahaifinshi, Mustafa Ozil ya fito yace dorawa dan nashi laifin fitar da kasar Jamus daga gasar cin kofin Duniya ba adalci bane, yace idan da shine Ozil kawai zai ajiye bugawa kasar tashi kwallone.

Yace da ace anyi nasara za'ace gaba dayan 'yan wasane da 'yan kasar suka samu nasara amma da yake yanzu an samu rashin nasara sai aka dorawa Ozil.

Mahaifin na Ozil yace ba dole sai dan nashi ya fito ya kare kanshi daga zarge-zargen da ake mishi ba dan a bayyane take cewa shekaru tara ya shafe yana bugawa kasar tashi kwallo kuma an samu nasarori kala-kala dashi.

A kan maganar daukar hoto da Erdogan kuwa, Mustafa yace, ba wani abu bane dan dan nashi yayi hakan, saboda shi mutum ne me kunya da girmama mutane, babban mutum kamar Erdogan bazai bukaci su dauki hoto tare ba yace a'a.

Ya kara da cewa, idan da a son ranshine ba zai baiwa dan nashi shawarar daukar hoton da Erdogan ba, amma ya tabbata daukar hoton bashi da wata alaka da siyasa dan ba wannan ne karin farko da suka dauki hoto tare ba.

No comments:

Post a Comment