Wednesday, 11 July 2018

'Yan kwallo 6 da ake kyautata zaton zasu maye gurbin Cristiano Ronaldo

Mun ji labari cewa ta tabbata babban ‘Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo ya tashi ya koma Kungiyar Juventus ta kasar Italiya bayan yayi shekaru kusan 10. Yanzu dai an fara maganar wadanda ake sa rai za su maye wurin ‘Dan wasan.


Daga cikin manyan ‘Yan wasan da ake sa rai za su maye wurin tsohon ‘Dan wasan Real Madrid Ronaldo da ya ci kwallaye sama da 450 a cikin shekara 9 akwai babban ‘Dan wasan gaban Brazil Neymar da kuma Takwaran sa na kasar Faransa, Mbappe wanda duk suke bugawa PSG wasa da 'yan kasar Belgium, Hazard da Lukaku.

1. Neymar Jr.

Ba mamaki Real ta nemi tsohon ‘Dan wasan gaban Barcelona Neymar Jr. ya toshe kafar da Ronaldo ya bari. Tun Neymar yana karamin yaro Real ke sha’awar ‘Dan wasan da yanzu ya fi kowa tsada a Duniya wanda yanzu yake PSG.

2. Eden Hazard

Akwai yiwuwar Real Madrid ta yi kokarin sayen ‘Dan wasan gaban nan na Kasar Belgium Eden Hazard. Hazard wanda kwanan nan aka cire kasar sa daga Gasar cin kofin Duniya yana takawa Kungiyar Chelsea ta Ingila leda ne a halin yanzu.

3. Kylian Mbape

Tun a bara aka yi tunani Real Madrid za ta nemi ‘Dan wasan gaban nan Kylian Mbape. Matashin ‘Dan kwallon ya koma PSG ne a matsayin ‘Dan kwallon aro kafin a saye sa bana kan kudi masu tsada kuma ba mamaki don ya dawo Kasar Sifen.

4. Remolu Lukaku.

Akwai kuma sabbin rahotannin dake cewa Real Madrid na neman dan wasan gaba na Manchester United, Remolu Lukaku a kokarinsu na samo wanda zai maye Cristiano Ronaldo bayan da ya koma Juventus, Kamar yanda Don Balon ta ruwaito.

Idan dai Lukakun yaje Madrid to ana tunanin zai rika sa ana ajiye Karim Benzema a benchi.

5. Harry Kane.

Dan wasan kasar Ingila me bugawa kungiyar Tottenham shima anyi rade radin cewa kungiyar Real Madrid na neman sayenshi, amma masu sharhi na ganin ba karamin kudi Madrid zasu sakarwa kungiyar Tottenham ba kamin su yarda su saki dan wasan.

6. Gareth Bale.

Masu sharhi na ganin cewa dan wasan Real Madrid din Gareth Bale zai iya samun walwala yanzu ya buga kwallo sosai fiye da daa lokacin Ronaldo na nan, dan kuwa dama can akwai alamar gasa a tsakanin 'yan wasan, duk da cewa Ronaldon ya mai fintin kau.

Bale dai yayi fama da samun ciwo akai-akai a kungiyarn amma ganin yanda yayi kokari wajan cin kwallaye a gasar cin kofin zakarun turai da Madrid din ta lashe, ana mai kyakkyawan zato.

No comments:

Post a Comment