Wednesday, 11 July 2018

'Yan sanda sun harbeni, sun mareni, sunce an aikosu su kasheni>>Inji gwamna Fayose a wani bidiyo da aka nunashi yana kuka

Wani faifan bidiyo daya bayyana, anga gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya bayyana yana kuka, yana fadin cewa jami'an tsaro a jihar tashi sun gaya mishi cewa, an aikisu su kasheshine.


Ya kara da cewa, sun gayamai suna da sakamakon zaben da zasu bayyana wa mutane wanda zai ba dan takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar APC nasara, sun kuma mareshi sun harbeshi, a ina ake irin wannan abu, yana gwamna guda ana mai irin wannan wulakanci?, kamar yanda ya fada.


Gwamnan yayi kira ga kungiyoyin kare hakkin bil'adama na Duniya dasu kawo dauki jihar ta Ekiti dan abinda yake faruwa ya wuce misali, ya kuma yi kira ga jama'ar jihar kada su karaya su ci gaba da tsayuwa tsayin daka dan ganin sun kada kuri'unsu, yace, yanzu zai koma asibiti dan a kula da lafiyarshi.

A cikin bidiyon da gwamnan ke jawabi an ganshi sanye da irin abin wuyarnan da ake sakawa marasa lafiya.

No comments:

Post a Comment