Monday, 2 July 2018

'Yan sanda sun yi zanga-zanga a Maiduguri

'Yan sanda sun yi zanga-zanga a gaban ofishin rundunar 'yan sandan jihar Borno da ke birnin Maidiguri.


Wasu mazauna birnin na Maiduguri sun shaida wa BBC cewar 'yan sandan sun tsayar da zirga-zirgar ababen hawa a kan titin da ke tsakanin rundunar 'yan sandan da ke kwalejin kimiyya da fasaha ta Ramat a birnin.

"A lokacin da suka fara zanga-zangar, sun yi ta harbi sama," in ji wani mazaunin garin.

Rahotanni dai sun ce 'yan sandan sun yi zanga-zagngar ne domin rashin biyan su wasu alawus-alawus da aka saba ba su game da yakin da ake yi da kungiyar Boko Haram.

Sai dai duk kokarin da BBC ta yi don jin ta bakin 'yan sandan da ke zanga-zangar da kuma rundunar 'yan sandan jihar kan dalilin hakan ya ci tura.

Wasu kafafen watsa labarai sun ruwaito cewar rundunar 'yan sandan jihar ta ce tana sane da matsalar kuma tana kokarin shawo kanta.

Ba safai ake ganin zanga-zangar jami'an tsaro irin su 'yan sanda ba a Najeriya.
BBCHausa.

No comments:

Post a Comment