Saturday, 14 July 2018

YUNKURIN BARIN APC: Oshiomole Ya Gana Da Kwankwaso Da Tambuwal

Sabon shugaban jam'iyyar APC, Kwamared Adams Oshiomole ya gana da tsohon gwamnan Kano Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da kuma gwamnan ihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal.


Wannan ganawar ta zo ne a yunkurin da sabon shugaban jam'iyar yake yi domin sasantawa da 'yan jam'iyyar wadanda suka yi yunkurin barin jam'iyyar.

Kafin ganawar tasa da Kwankwason da kuma Tambuwal, Shugaban ya gana da shugaban majalisar Dattawa da na majalisar Wakilai wato Sanata Bukola Saraki da Yakubu Dogara dama sauran manyan 'yan jam'iyyar ta APC a majalisun guda biyu duk a kokarin sa na sasantawa don su janye yunkurinsu na barin jam'iyyar

Daga Real Sani Twoeffect Yawuri

No comments:

Post a Comment