Thursday, 12 July 2018

Zamu yi kwallon ko a mutu ko ai rai dan ganin munci kofin Duniya>>Mbappe

Tauraron dan kwallon kafar kasar Faransa wanda akewa kallon yana daya daga cikin na gaba-gaban wanda zasu gaji Cristiano Ronaldo a kungiyar Real Madrid, Kylian Mbappe ya bayyana cewa baya kokarin yin gasa da Ronaldon wajan cin kyautar Ballon d'Or.


Mbappe ya bayyanawa manema labarai cewa, ba kokarin cin Ballo  d'Or bane a gabanshi, abinda yake son gani ya ci shine kofin Duniya, yana so yayi bacci dashi, zai yi duk abinda ya kamata, kai zamu kashe kanmu waja  ganin mun dauki wannan kofi.

Ya bayyana hakane bayan da Faransar ta kai wasan karshe a gasar cin kofin Duniya 2018.

A wani labarin kuma, tsohon me horas da 'yan kwallon Arsenal, Arsene Wenger, wanda kadan ya rage ya sayi Mbappe kamin Monaco su sayeshi, ya bayyana cewa, matashin dan wasan yana buga kwallon huce takaici, idan ya dauki kwallo to na tabbata zai yi wani abin birgewa.

Wenger ya kara da cewa kallon kwallon Mbappe tana sakashi cikin farin ciki sosai.

No comments:

Post a Comment