Thursday, 16 August 2018

A karo na biyu, Ronaldo ya sake ciwa Juventus kwallo

A yayin da Real Madrid ta buga wasanta na farko babu Cristiano Ronaldo kuma tayi rashin nasara a hannin Atletico Madrid daci 4-2, Ronaldon ya sake ciwa sabuwar kungiyarshi ta Juventus kwallo a karo na biyu tun bayan komawarshi kungiyar.


A wani bidiyo da kungiyar ta Juventus ta wallafa wanda ya nuna manyan 'yan kungiyar na bugawa wasan atisaye da matasan 'yan kungiyar 'yan kimanin shekaru 23, anga Ronaldo ya ci wata kayatacciyar kwallo.

Mutane da dama sun jinjinawa Ronaldon akan wannan bajinta da ya nuna.

Ranar Asabar ne idan Allah ya kaimu Ronaldon zai bugawa Juventus wasan farko da wata kungiya ta daban.

No comments:

Post a Comment