Wednesday, 1 August 2018

A ranar 1 ga Agusta dokar hana sanya Hijabi za ta fara aiki a Denmark

Daga yau, 1 Agusta dokar hana sanya Hijabi za ta fara aiki a Denmark inda tuni mata da ke saka Hijabin suka shirya gudanar da zanga-zanga.


Kamar yadda ya ke a wasu kasashen Turai Denmark ma ta hana sanya Hijabi a ma'aikatu da hukumomin gwamnati.

Mata na shirin gu─▒danar da zanga-zangar adawa da wannan doka da za ta fara aiki a ranar 1 ga Agusta.

Mata da yawa a kasar da suka hda da masu sanya Hijabi da ma wadanda ba sa sanyawa ne za su gudanar da zanga-zangar.

A karkashin dokar an daina saka Hijabi zurmeme, Nikabi ko wani wabu da zai rufe fuska da kuma makala gemun gangan.

Dokar ta ba wa 'yan sanda damar hana matan da suka ki cire Hijabinsu shiga ma'aikatun gwamnati.

Za a iya cin tara har ta dala dubu 1,600 ga matan da suke saka Hijabin.
TRThausa.

No comments:

Post a Comment