Sunday, 12 August 2018

ABIN AL'AJABIN DA YA AUKU A YAYIN ZABEN SANATAN BAUCHI TA KUDU

Wani abin Al'ajabi daya faru a wata mazaba a Jihar Bauchi a yayin zaben cike gurbi da ya gudana a yau Asabar 11/8/2018 inda wasu gungun mata masu zabe suka dinga kiran "Sai Baba Buhari kafin su jefa kuri'unsu tareda sunbatar katin zaben.


Kamar yadda kamfanin dillancin labaran Nijeriya ya ruwaito wato (NAN) yace al'amarin ya faru ne a mazabar Veterinary dake gundumar Dawaki a kwaryar birnin jihar ta Bauchi inda wasu mata hudu suka dinga ambaton sai Baba kuma suna sumbantar katin zaben kafin su jefa kuri'un.

Wannan abin dai ya sa wasu suna tsammanin cewar ko matan sun dauka zaben shugaba Muhammadu Buhari ake yi a madadin zaben da ainihi ake yi na cike gurbi a yankin Bauchi ta kudu.

Ita dai kalmar sai Baba wata kalma ce magoya bayan Shugaba Muhammadu Buhari suke amfani da ita a yayin gamgamin siyasa.

Da kamfanin dillacin labaran na Nijeriya ya so ya ji ta bakin Matan sun ki suyi magana akai.

Da ake zantawa da wata ma'aikaciyar rumfar zaben tace wannan karon an samu fitowar mata da yawa a yayin zaben cike da shaukin son jefa kuri'unsu.
Daga Real Sani Twoeffect Yawuri

No comments:

Post a Comment