Monday, 27 August 2018

Abin da ya sa Buhari ba zai yi wa Trump raddi ba

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ba zai ce uffan ba kan kalaman da aka ambato shugaban Amurka Donald Trump ya yi a kansa.


Jaridar Financial Times ta Burtaniya ce ta wallafa labarin da ke cewa Shugaba Trump ya bayyana Shugaba Buhari a matsayin mutum mara kuzari.

Ta ce shugaban ya shaida wa wasu majiyoyinta cewa "har abada ba ya son sake ganawa da Shugaba Buhari saboda ba shi da kuzari."

Sai dai kakakin shugaban kasar, Mr Femi Adesina, ya gaya wa BBC cewa ba za su ce uffan a kan batun ba saboda ba shi da tushe bare makama.

A cewarsa, "A matsayinku na 'yan jarida kun san cewa duk jaridar da ta ambato majiya maras tushe, ba da gaske take ba. Don haka ba zan ce komai a kan wannan batu ba."

Mr Adesina bai tsaya wakiliyar BBC ta gama yi masa tambaya ba, sai ya katse wayarsa.
Batun dai ya jawo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta na Najeriya, inda wasu ke yi wa Shugaba Buhari shagube bisa kalaman da Mr Trump ya yi.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment