Thursday, 30 August 2018

Abin dariyane hana Ronaldo gwarzon UEFA: Salah ya Share Ramos

Da alama dai ta bangaren Cristiano Ronaldo, rashin samun kyautar gwarzon UEFA 2017/18 bai musu dadiba kwata-kwata domin wakilinshi Jorge Mendes ma ya bayyana cewa ba'awa gwamnin nashi adalci ba.


Ronaldo dai yaki zuwa wajan bayar da kyautar ta UEFA bisa zargin rashin adalci da aka mishi na kin bashi kyautar gwarzon shekara, kamar dai yanda aka sani, dan wasan ba ya son zamowa na biyu a duk wata gasa da ya shiga.

Wakilin Ronaldon Mendes ya bayyana cewa rashin baiwa Ronaldon kyautar abin dariyane da kuma takala.

Mendes ya bayyanawa, kafar watsa labarai ta Records cewa, Ronaldo yaci kwallaye 15 a gasar sannan ya goya Real Madrid a bayanshi ya kaisu ga nasara amma ace wai bashine ya ci wannan kyautaba.

Game da rashin halartar dan wasan gurin bayar da kyautukan kuwa, tsohon abokin aikinshi, Sergio Ramos ya bayyana cewa, sunyi mamaki da basu ganshi ba amma Ronaldon ya kan yi abinda yake sone a lokuta da dama.

Wani abu da ya dauki hankulan mutane a lokacin bayar da kyautar shine yanda bayan Dan wasan baya na Real Madrid Sergio Ramos ya amso kyautarshi ta gwarzon dan wasan baya na UEFA ya shafa kafadar Mohamed Salah wadda a karon battar da sukayi lokacin wasan karshe na cin kofin UEFA Champions League ta yi sanadin karye warshi.

Saidai yayin da Luka Modric ya baiwa Ramos hannu suka gaisa ya kuma tayashi murna, Salah ya ci gaba da kallon gabanshi be kula Ramos ba.

Wannan abu ya dauki hankulan mutane.

No comments:

Post a Comment