Monday, 20 August 2018

Abinda shugaba Buhari yake nufi da ‘cigaba da kama barayi’>>Kaakakin gwamnati

Babban hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bangaren watsa labaru, Femi Adesina ya yi karin haske game da batun da Buhari ya furta jim kadan bayan dawowarsa daga kasar Landan game da kama barayin gwamnati.


Isar fadar gwamnati, shugaba Buhari ya bayyana ma wani dan jarida cewa zai cigaba da kama barayin gwamnati, wadanda suka karya tattalin arzikin Najeriya a baya, kamar yadda.

Sai dai Femi yayi karin haske a cikin wata hira da yayi da gidan talabijin na Channels, inda yace barawo ne kadai zai razana da wannan batu na shugaba Buhari, ko kuma mutanen dake nufin sata.

Haka zalika Femi yace duk cecekucen da ake yi game da wannan batu na Buhari bai dadasu da kasa ba, masu suka su yi tayi, su kam ko a jikinsu wai an tsikari kakkausa, inji shi, “Kasan jama’a zasu yi ta neman matsalar mutum, kai wasu ma idan aka kaisu Aljann sai sun ci gyara.”

“Game da maganan kama barayi, barayi ne da masu son in sata ne kadai zasu razana, saboda mun sani a baya sata ba rashawa bane, amma a yau sata rashawa ne, don haka duk wanda aka kama yayi kuka da kansa.” Inji Femi Adesina.
Naija.ng.

No comments:

Post a Comment