Sunday, 26 August 2018

Abu daya kawai PDP zatayi ta kada Buhari>>Makarfi

Dan takarar shugabancin kasa a karkashin jam'iyyar PDP, Sanata Ahmed Makarfi ya gargadi jam'iyyarsa ta PDP cewa dole su tsayar da dan takara mai nagarta da farin jini muddin suna son kayar da shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019.


The Nation ta ruwaito cewa Makarfi ya gargadi masu ruwa da tsaki a jam'iyyar PDP cewa har yanzu shugaba Muhammadu Buhari yana da farin jini sosai a yankin arewa kuma yankin ne tafi sauran yawan masu kada kuri'a.

Makarfi wanda tsohon Ciyaman din rikon kwarya na PDP ne ya ce ya zama dole jam'iyyar PDP ta yi kokarin sauya tunanin masu zabe a yankin arewa saboda har yanzu mafi yawancinsu 'yan a mutun shugaba Muhammadu Buhari ne.

Rahoton ya ce Makarfi ya yi wannan maganar ne a ranar Juma'a yayin wata taro da ya yi deleget din jam'iyyar PDP na jihar Ekiti karkashin jagorancin mataimakin gwamna, Farfesa Kolapo Olusola a kokarinsa na kamfen din samun tikitin takarar shugabacin kasa gabanin taron jam'iyyar.

Makarfi ya yi alkwarin zai magance matsalar rashin tsaro, rashin ayyukan yi, matsalar wutan lantarki da sauran matsalolin da ke adabar Najeriya muddin aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.

"idan muna son muyi nasara a zaben 2019, kar mu sake mu rasa kuri'un mutanen arewa kuma dole mu dan takarar da zasu amince dashi.

"Matsalar mu shine lashe zabe a arewa, shugaban kasa mai ci yanzu dan arewa ne kuma jama'a sun matukar kaunarsa. Idan muna son muyi nasara sai mu fitar da dan takara daga arewa.

"Dole mu yi kokarin sauya tunanin 'yan gani kashe nin Buhari domin su karkato zuwa gare mu."
Naija.ng.

No comments:

Post a Comment