Sunday, 12 August 2018

Abu ne me matukar wuya Ganduje ya sake cin zabe a Kano>>Tsohon mataimakin gwamna Hafiz Abubakar

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafiz Abubakar ya bayyana cewa lura da irin yanda abubuwa ke gudana a siyasar jihar Kano, abune me matukar wuya ace Ganduje ya sake cin zabe a shekarar 2019.


Farfesa Hafiz yayi wannan bayanine a lokacin da yake hira da jaridar The Punch.

Ya kara da cewa, PDP ce zata samu nasara a jihar a zabe me zuwa domin kuwa da yawa wanda ke zagaye da gwamnan sun gaji da zama a APC saboda rashin adalcin da ake musu suna ta komawa PDP.

Yace 'yan majalisar jihar ma ba'a barsu a bayaba wajan canja shekar inda ya kara da cewa yana da yakinin tsohon gwamnan jihar, Sanata Kwankwasone zai samu tikitin tsayawa takara a PDP.

No comments:

Post a Comment