Wednesday, 8 August 2018

Abubuwa 3 da zasu iya faruwa kamin shugaba Buhari ya dawo Najeriya

1. Tsige Bukola Saraki

Babu mamaki idan har an bude Majalisa ayi yunkurin tsige Bukola Saraki bayan ya koma Jam’iyyar PDP wanda ba ta da rinjaye a Majalisa. Jam’iyyar APC mai mulki tuni ta gama zawarcin Sanata Godswill Akpabio da ake tunani zai ja ragamar Majalisar Dattawan kasar.

2. Tantance Shugaban EFCC

Idan har an nada wani sabon Shugaban Majalisar Dattawa, babu mamaki fadar Shugaban kasa ta kara aikawa Majalisar sunan Ibrahim Magu domin a tabbatar da shi a matsayin mukaddashin Shugaban EFCC. A baya dai Hukumar DSS ta nemi kar a dakatar da Magu.

3. Nadin sababbin mukamai da sauran su

Babu mamaki dai kafin Shugaban kasa Buhari ya dawo a nada sabon Shugaban DSS. Kuma da zarar an bude Majalisa, fadar Shugaban kasa za ta nemi a tabbatar da wasu nade-nade da ke gaban Majalisa. Akwai kuma batun kasafin kudin bana da ake sa rai a gama aikin sa.

No comments:

Post a Comment