Friday, 3 August 2018

Ahmed Musa ya koma kungiyar Alnassr ta kasar Saudiyya daga Leicester

Tauraron dan kwallon Najeriya, Ahmed Musa ya koma kungiyar kwallon kafa ta Alnassr dake kasar Saudiyya daga tsohuwar kungiyarshi ta Leicester United dake kasar Ingila akan kudi Yuro miliyan 16.


Kungiyar ta Alnassr ta bayyana cewa Musa ya dawo kungiyar tata akan kwantirakin buga mata wasa na tsawon shekaru 4 sannan kuma ta mishi barka da zuwa.

Musa ya haskaka a gasar cin kofin Duniya da akayi a kasar Rasha inda ya ci kwallaye 2.

Alnassr doke kungiyoyi da dama wajan sayen Musa da ga Leicester, muna tayashi murna.

No comments:

Post a Comment