Sunday, 19 August 2018

A'isha Alhassan, Mama Taraba ta tsallake rijiya da baya yayin da wasu sukayi yunkurin hallakata

Wasu rahotanni sun bayyana cewa, ministar harkokin mata, A'isha Alhassan wadda aka fi sani da Maman Taraba ta tsallake rijiya da baya, rahotannin dai sun ce, wasu ne sunka yi yunkurin hallaka ta amma Allah ya taimaketa ta tsira.Shafukan Voice of Liberty dana Labarun Siyasa duk sun wallafa wannan rahoto inda suka wallafa hotunan motocin da aka lalata.

A kwanakin bayane dai Maman Taraba ta bayyana cewa zata sake tsayawa takarar gwamnan jihar a zaben shekarar 2019 idan Allah ya kaimu.

No comments:

Post a Comment