Sunday, 26 August 2018

AIYUKAN DA AKE SAMUN LADAN HAJJI

IDAN ALLAH BAI HORE MAKA ZUWA
HAJJI BA, KADA KA DAMU GA WASU AIYUKA DA SUKA TABBATA A SUNNAH IDAN AN YI SU ANA SAMUN LADAN HAJJI, AMMA BA SA TSAYAWA A MATSAYIN HAJJI, SAI SAMUN LADA KAMAR AN YI HAJJI.


NA DAYA: DUK MUTUMIN DA YAKE SALLAH A JAM'I, YANA SAMUN LADAN HAJJI A KOWACCE SALLAH , DUK WATA ZAI SAMI LADAN HAJJI 150, SAHIHUL JAMI'I 6006.

NA BIYU: DUK WANDA YA YI SALLAR ASUBA A CIKIN JAM'I, YA ZAUNA YANA AMBATON ALLAH HAR RANA TA FITO, SANNAN YA YI SALLAH RAKA'A BIYU, YANA DA LADA KAMAR YA YI HAJJI DA UMRA. SAHIHUL TARGEEB 46.

NA UKU: DUK WANDA YAKE TASBIHI 33 TAHMID 33 KABBARA 33, ZAI KAMO WADANDA SUKA BIYA KUDI SUKA JE HAJJI A WAJEN LADA.  BUKHARI DA MUSLUM 

NA HUDU: DUK WANDA YA YI SAMMAKO ZUWA MASALLACI BA YA NUFIN KOMAI SAI KOYAN ALKAIRI KO YA SAMI WANI ILMI, YANA DA LADA KAMAR YA YI HAJJI CIKAKKA. SAHIHUL TARGEEB 86.

NA BIYAR: DUK WANDA YA YI UMRA A WATAN RAMADAN KAMAR YA YI HAJJI. BUKHARI DA MUSLUM.

NA SHIDA: DUK WANDA YA DAUKI NAUYIN WANI YA YI HAJJI KO YA BAWA WANI GUZURIN AIKIN HAJJI,  SHI MA KAMAR YA YI AIKIN HAJJI. SAHIHUL TARGEEB 1078

NA BAKWAI: DUK WANDA YA YI NIYAR AIKIN HAJJI, SAI WATA LARURA TA TARE SHI WADDA TA FI KARFIN SA, ZAI SAMI LADAN AIKIN HAJJI SABODA LADAN NIYYA. BUKHARI DA MUSLUM. 

ALLAH YA KARBI HAJJINMU YA KARAWA KASARMU ARZIKI DA ZAMAN LAFIYA.
Daga Malam Aminu Ibrahim Daurawa

No comments:

Post a Comment