Thursday, 23 August 2018

Albarkacin babbar Sallah: Gwamna Ganduje ya saki 'yan gidan yari 170

A wani mataki na bukukuwan Sallah da rage cinkoso a gidajen yarin kasarnan, gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya saki masu zaman gidan yari akan laifuka daban-daban da suka aikata har su 170.


Bayan sakin nasu, gwamnan ya kuma baiwa kowannensu kudin mota, naira 5000 dan su yi amfani dasu zuwa gidajensu.

Gwamnan ya bayyana wannan mataki da cewa ci gabane na shirin gwamnatin tarayya na kokarin da take na rage cinkoso a gidajen yarin kasarnan, ya kuma ce, shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bukaci gwamnoni da su taimaka wajan rage cinkoso a gidajen yarin kasarnan.

Ya kuma yi kira ga wadanda aka saka din da cewa su gujewa aikata laifikan da zasu sa a sake mayar dasu gidan yarin.

No comments:

Post a Comment