Thursday, 16 August 2018

Ali Nuhu Ya Zama Jakadan Yaki Da Miyagun Kwayoyi

Tauraron fina-finan Hausa, Ali Nuhu, Sarki ya samu jakadancin yaki da miyagun gwayoyi daga wata gidauniya me suna Big Church Foundation, a sakon daya fitar ta dandalinshi na sada zumunta, Ali yace, wannan ba karamin abin girmamawa bane.Ga sakon daya fitar ta dandalinshi na sada zumunta kamar haka:

"Abin girmamawa ne da aka bayyana ni a matsayin Jakada a kan yaki da  shan miyagun kwayoyi a ƙarƙashin Babba Gidauniyar nab ta “Big Church  Foundation”. Wannan babban aiki ne amma dole mu fara ta wani wuri idan muna bukatar al’umma tagari. ku zo mu hada kai", cewar Ali Nuhu.

No comments:

Post a Comment