Friday, 17 August 2018

Alkawuran Da Shugaba Buhari Ya Daukarwa 'Yan Nijeriya Yayin Yakin Neman Zabe Kuma Ya Cika Su

1- Buhari ya yi alkawari zai yi fada da kungiyan Boko Haram zai kuma inganta tsaro ya kuma cika alkawari mun gani mun shaida.


2- Ya yi alkawari zai yi fada da cin hanci da rashawa yana kan yi muna gani da idanun mu mun kuma shaida mun gamsu.

3- Ya yi alkawari ba zai cuce mu ba kuma ba zai bari a cuce mu ba. Haka yake mun shaida.

4- Ya yi alkawari zai dawo da martabar Nijeriya a idon duniya gaskiya ne mun shaida.

5-Ya kuma ce zai farfado mana da tattalin arzikin kasar mu Nijeriya. Idan ba a manta ba gwamnatin da ta shude sai da ta yi kaca-kaca da kasar kafin Buhari ya karba.

Allah ya dafawa gwamnatin Buhari Ya kare mana shi daga sharrin makiya da azzalumai wadanda ba su san ciwon kan suba kuma ba sa son cigaban Nijeriya.
Daga Baffah Abubakar

No comments:

Post a Comment