Tuesday, 28 August 2018

Allah ka bani miji wanda yasan gyaran Gado>>Inji wannan budurwar

Mata harma da maza sukan yi addu'o'in samun abokan zama na gari, a wasu lokutan mutum yakan ce ga kalar wanda yakenso ya samu a matsayin abokin zama, wata baiwar Allah ta bayyana irin mijin da take son samu wanda ya dauki hankulan mutane akai ta sharhi akai.

Baiwar Allahn ta bayyana a dandalinta na sada zumunta cewa, Allah ka bani miji na gari, me hankali wanda yasan gyaran Gado. Amin.

Kalmar da tayi ta cewa, wanda yasan gyaran Gado ya dauki hankulan mutane inda wasu suka rika tambayarta da me take nufi da haka, wasu kuwa cewa sukayi, ita gyaran gadone matsalarta? 

No comments:

Post a Comment