Saturday, 18 August 2018

An kai hari Masallatan Juma'a 2 a Ingila

An kai hare-hare har sau 2 a jere a wasu Masallatan Juma'a 2 da ke garin Bermingham na Kasar Ingila.


Sanarwar da aka fitar ta ce, an kai harin a Masallatan da ke yankunan da suke da Musulmai da yawa.

Sanarwar ta ce, an kai hari na farko da karfe 22.00 a Masallacin Kamarul ─▒slam a lokacinda ake Sallar Isha'i inda aka kai na biyu bayan mintuna 20 aka kai a Masallacin Al-Hijra.

'Yan sandan Bermingam sun ce, an farfasa gilasan masallatan a lokacinda aka kai harin kuma an kai jami'an kashe gobara da yawa.

An fara bincike game da harin da ba a jikkata kowa ba.

Al'umar Musulmin Ingila sun la'anci harin.
TRThausa

No comments:

Post a Comment