Tuesday, 7 August 2018

An kama shugaban hukumar DSS, Lawal Daura bayan saukeshi daga mukaminshi

Rahoton Sahara Reporters na cewa, bayan sauke shugaban hukumar 'yan sandan farin kaya, Lawal Daura, jami'an 'yan sanda sun kamashi saboda zargin yiwa harkar tsaron kasa katsalandan.


A Safiyar yaune dai jami'an na 'yan sandan farin kaya suka tare kofar shiga majalisar tarraya inda suka hana 'yan majalisar shiga gurin aikinsu.

Mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo yayi ganawa da shugaban hukumar DSS inda daga baya ya tsigeshi daga mukaminshi.

No comments:

Post a Comment